
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Yadda Ilimi Ke Kara Tsada Yayin Komawar Yara Makaranta
•
Idris Daiyab Bature
Iyaye na ci gaba da kokawa kan yadda ilimi ke kara tsada yayin komawan yaransu makaranta a sabon zango.
Makarantu na kara fidda sabbin hanyoyin karbar kudi daga hannun yara da sunan koyarwa.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan dake sa ilimi kara tsada yayin da yara ke komawa makaranta.