
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Rayukan Da Aka Rasa Sakamakon Ambaliyan Wannan Shekarar
•
Idris Daiyab Bature
Duk shekara rayuka da dukiyoyi na kara salwanta sakamakon ambaliyar ruwa.
Duk da jan kunne da hukumomi a matakai daban-daban keyi, rayukan mutane da dukiyoyi na kara salwanta.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan rayukan da suka salwanta a damunan wannan shekarar.