Najeriya a Yau

Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin Ribas?

Idris Daiyab Bature

Send us a text

A yau ne Gwamna Siminalaye Fubara ke dawowa kujerarsa a matsayin gwamnan Jihar Ribas bayan dakatarwa da ayyana dokar ta baci na watanni shidda da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a jihar.


Manazarta dai na hasashen wannan dawowar zata bude wani sabon babi a siyasar jihar Ribas.


Yayin da wasu ke ganin gwamna Fubara zai koma bakin aiki ne ya cigaba da gudanar da mulkin jihar kamar yadda ya barta, wasu kuwa gani sukeyi akwai babban kalubale dake gaban gwamnan.