Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Dalilan Da Suke Sa Dalibai Cin NECO Fiye da WAEC
•
Idris Daiyab Bature
Yayin da dalibaI da dama da suka rubuta jarrabawar kammala karatun sakandare suka fitar da zaton samun gurbi a makarantun gaba a bana bisa la’akari da sakamakon WAEC, sai ga sakamakon NECO ya taho musu da sabon albishiri.
Yayin da sakamakon WAEC ya bar baya da kura, inda galibi suka kasa samun makin da ake bukata a mafi karancin adadin darussa, na NECO ya yi nuni da cewa galibi sun tsallake wannan siratsi.
Ko wadanne dalilai ne sukan sa wasu dalibai faduwa jarrabawar WAEC amma su samu ta NECO?
Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.