Najeriya a Yau

Me Ya Sa Mutane Suka Dawo Daga Rakiyar Kirifto?

Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Send us a text

A ’yan watanni da suka gabata, matasa da yawa a Najeriya sun dukufa don ganin hakar su ta cimma ruwa wajen samun kudaden kirifto.

Amma alamu na cewa a baya-bayan nan wasu daga cikinsu sun sare sun kuma saduda sun dawo daga rakiyar harkar.

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan dalilan wasu matasan na yin watsi da harkar kirifto.