
Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Shin Babu Wata Hanyar Magance Matsalolin ASUU Ne Sai Ta Yajin Aiki?
•
Idris Daiyab Bature
Shekara da shekaru kungiyar malaman jami’oi ASUU ta kwashe ta na gudanar da yajin aiki ba tare da samun biyan bukata ba.
Irin wannan yajin aiki da kungiyar malaman ke shiga ya jefa dalibai da malaman da ma harkar ilimi cikin halin ni ‘yasu a Najeriya.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wasu hanyoyin da kungiyar malaman ASUU za ta iya bi don warware matsalar ta ba tare da dogaro da gwamnatin tarayya ba.