Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Shin Ya Kamata A Saki Shugaban IPOB Nnamdi Kanu?
•
Idris Daiyab Bature
Tun bayan fara shari’ar Nnamdi Kanu a shekarar 2021 mutane da dama suke bayyana ra’ayoyinsu a kan sake shi ko a kyale shari’a ta yi halinta.
Hasali ma har zanga-zanga wasu ‘yan Najeriya suka kira don bayyana bukatar sakin shugaban na ‘yan aware.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan ko ya dace a saki Nnamdi Kanu?