Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Halin Da Muka Shiga Sakamakon Haihuwar ‘Ya Mai Cutar Motsewar Kwakwalwa
•
Idris Daiyab Bature
Cutar Cerebral Palsy, wadda ake kira Ciwon tsukewar kwakwalwa, na daga cikin manyan matsalolin lafiyar yara da ke tasowa tun daga haihuwa. Wannan cuta tana faruwa ne sakamakon rauni ko lalacewar wani ɓangare na kwakwalwa da ke kula da motsi, magana, da daidaiton jiki.
A mafi yawan lokuta, cutar tana bayyana ne tun daga ƙuruciya, a wasu lokutan kuma kamar yadda masana kiwon lafiya suka bayyana, cutar na faruwa ne tun kafin a haifi yaro.
Ko ta wadanne irin hanyoyi wannan cuta take kama yaro?
wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.