Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Shin Ko Sauya Hafsoshin Tsaro Zai Kawo Karshen Aikin Ta’dda A Najeriya?
•
Idris Daiyab Bature
Tun bayan sauya hafsoshin tsaro da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ne dai mutane da dama keta tofa albarkacin bakinsu, yayin da wasu ke ganin hakan zai taimaka wajen yaki da rashin tsaro, wasu kuwa na ganin duk jama’ar ja ce.
Shin ko sauya hafsoshin tsaro zai kawo karshen fargaban da al’umma ke yi?
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari akai.