Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Ko Kawo Dakarun Kasar Amurka Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya?
•
Idris Daiyab Bature
Ana ta ce-ce- ku-ce kan batun da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na kawo dakarun kasar sa Najeriya don taimakawa wajen yaki da matslar tsaro.
Yayin da wasu ke ganin hakan abun san barka ne, wasu kuwa tofin Ala tsine suka yi ga wannan batu.
Shin ko me zai faru idan aka kawo dakarun kasar Amurka Najeriya don shawo matsalar tsaro?
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.