Najeriya a Yau

Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Cutar Basir

Idris Daiyab Bature

Send us a text

Cutar basir na daga cikin cututtukan da mutane da dama ke da mabanbantan ra’ayoyi akan ta.

A lokuta da dama za ka ji yadda mutane ke fadin dalilai daban daban da ke janyo cutar basir, yayin da wasu ke ganin yawan zama ne ke kawo ta, wasu kuwa gani suke yi zaki da maiko ne ke kawo ta.

Wannan shine abun da da yawa daga cikin mutane suka sani kan wannan cuta, sai dai masana kiwon lafiya na da nasu fahimtar daban kan wannan cuta.

Shirin Najeriya  A Yau na wannan lokaci zai tattauna ne kan cutar basir da hanyoyin magance ta.