Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Matsayar Doka Kan Taron Da Jam'iyyar PDP Ta Gudanar
Matsayar doka ta zama babbar abun tattaunawa a Najeriya yayin da jam’iyyar PDP ta gudanar da taron ta na kasa duk da mabanbantan hukunce hukunce daga kotuna biyu.
Umarnin kotu guda yana goyon bayan taron, ɗayan kuwa ya haramta shi gaba ɗaya. Wadannan hukunce hukunce ba baiwa jam’iyyar damar yi ko haramta musu taron kadai suka yi ba, harda baiwa hukumar zabe ta kasa umurnin saka ido ko haramta musu wannan dama yayin taron.
Duk da wadannan hukunce hukunce, jam’iyyar ta gudanar da taron inda ta zabi shugabannin da zasu cigaba da jan ragamar al’amuranta da kuma daukar wasu kwararan matakai.
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.