Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Waiwaye Kan Irin Gudunmawar Da Sheikh Dahiru Bauci Ya Bayar Ga Cigaban Addini
Sheikh Dahiru Usman Bauchi, fitaccen malamin addinin Musulunci, masanin tafsiri, kuma jagoran darikar Tijjaniyya, shahararre ne saboda iliminsa mai zurfi da tasirin da ya yi a fagen addini da tarbiyya a Najeriya da ma ƙasashen Yammacin Afirka.
Sheikh Dahiru Bauci ya shafe sama da shekaru saba’in yana koyar da ilimi, ya gudanar da tarukan tafsiri a duk shekara, ya gina makarantu, ya kafa cibiyoyi, kuma ya ba da ilimi ga dubban almajirai hanyoyin da suka taimaka wajen yaɗa ilimin addini cikin lumana da biyayya ga Allah Madaukakin Sarki. Rayuwarsa ta kasance tsantsa ta tsoron Allah, tawali’u, da ayyukan alheri.
A wannan waiwayen, za mu duba manyan abubuwa da suka yi fice a cikin rayuwar marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauci da irin tasirin sa ga al’umma, da darussan tafsirin Alƙur’ani da ya yi wa duniya, da irin irin kyawawan dabi’u da ya bari a matsayin abun gado ga musulmi.