Najeriya a Yau

Yadda Takunkumin Amurka Zai Shafi Tattalin Arzikin ‘Yan Najeriya

Idris Daiyab Bature

Send us a text

Takunkumin da Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, ya sanya wa wasu ‘yan Najeriya ya sake jawo hankali kan irin tasirin manufofin ƙasashen waje ga rayuwar mutane da tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya. 


Wannan takunkumi, wanda ya haɗa da hana shiga Amurka, da toshe kadarori ko hana mu’amala da wasu hukumomi da kamfanonin Amurka, ba wai hukunci ne ga mutum ɗaya kaɗai ba, kazalika yana da tasiri mai zurfi ga harkokin kasuwanci, zuba jari da martabar ƙasa a idon duniya.

Ko ta yaya wannan takunkumi zai shafi tattalin arzikin daidaikun wadanda abun ya shafa, da ‘yan uwansu da ma Najeriya baki daya?


Wannan shine batun da shirin Najeriya  A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.