Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Irin Asarar Da Aka Tafka A Kasuwar Kafintoci Dake Kano
•
Idris Daiyab Bature
Gobara a irin wannan yanayi na iska musamman a kasuwanni da gidaje ba sabon abu bane kuma ba abun mamaki ba. Wasu kafintoci dake aiki a kasuwar lale dake unguwar Tal’udu a karamar hukumar Gwale dake jihar Kano sun wayi gari da alhinin gobarar da ta yi sanadiyyar raba su da hanyar abincinsu.
Wannan gobara da ba’a san musabbabinta ba ta janyo asarar miliyoyin Naira tare da jefa wadanda abun ya shafa cikin mawuyacin hali.
Ko wanne irin hasara aka yi a wannan gobara?
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba akai.