Najeriya a Yau

Cushe-cushen Da Ake Zargin An Yi A Sabbin Dokokin Haraji

Idris Daiyab Bature

Send us a text

Takaddama mai zafi ta dabaibaye sabbin dokokin haraji da Majalisar Tarayya ta amince da su, bayan zarge-zargen cewa an samu sauye-sauye a cikin dokokin bayan an kammala dukkan matakan amincewa da su a majalisa. Batun da ya taso ya jawo cece-kuce daga ‘yan majalisa, jam’iyyun adawa da kungiyoyin fararen hula, inda suke tambayar sahihancin abin da aka mika wa Fadar Shugaban Kasa domin aiwatarwa.


Masu suka na cewa sauye-sauyen da ake zargin an yi ba tare da amincewar majalisa ba na iya lalata tsarin dimokuraɗiyya, tare da haifar da rashin gaskiya da amana a tsarin dokoki. A daya bangaren kuma, fadar shugaban kasa ta yi nuni da cewa abin da aka yi gyara ne na fasaha da tsari, ba sauya ma’anar doka ba.

Ko wadanne irin sauye sauye aka yiwa sabon dokar harajin?


Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.