Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Abin Da Ya Kamata Ku Yi Yayin Takaddama Da ’Yan Sanda
Babban alhakin da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya dora wa Rundunar ’Yan Sanda shi ne kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa.
Sai dai a lokuta da dama, akan samu fito-na-fito sakamakon zargin ’yan sanda da wuce gona da iri wajen gudanar da aiyyukan nasu.
Shirin Najeriya a Yau ya tattauna a kan yadda abubuwan da ya kamata ’yan kasa su yi idan ’yan sanda suka nemi cin zalinsu.