Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Hanyoyin Mallakar Gida Ga Mai Karamin Karfi
Mallakar muhalli na cikin burace-buracen kusan kowanne dan Najeriya.
Sai dai wadannan burace-burace, a galibin lokuta, ba sa cika – musamman ga masu matsakaitan samu.
Amma wasu masana suna ganin akwai dabarun da marasa karfi ma za su iya amfani da su don su mallaki nasu muhallin, daidai ruwa daidai tsaki.
A kan wadannan dabaru shirin Najeriya A Yau zai yi nazari..