Najeriya a Yau

Tasirin Yankan Al’aura A Rayuwar 'Ya'ya Mata

Use Left/Right to seek, Home/End to jump to start or end. Hold shift to jump forward or backward.

0:00 | 25:44

Send us Fan Mail


A tsakanin al’ummomi daban-daban akan samu wasu al’adu na yanke wani bangare na al’aurar ’ya’ya mata saboda wasu dalilai.

A kasar Hausa akan yi abin da ake kira yankan angurya da nufin rage wa mace sha’awa, musamman kafin ta yi aure.

Ko menene tasirin wannan al’ada a rayuwar ’ya’ya mata?

Albarkacin Ranar Yaki da Yankan Al’aurar Mata ta Duniya, shirin Najeriya  A Yau zai yi nazari a kan wannan batu.