Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Dabarun Bunkasa Kasuwanci A Intanet
Use Left/Right to seek, Home/End to jump to start or end. Hold shift to jump forward or backward.
Masu iya magana kan ce “zamani riga”.
Sauyin zamani ya kawo sauye-sauye da dama a yadda ake gudanar da harkoki, ciki har da kasuwanci.
A yanzu haka, zamani, intanet na taka muhimmiyar rawa wajen tallata haja ko saye da sayarwa.
Shrin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan dabarun da za ku iya amfani da su don bunkasa kasuwancinku ta hanyar amfani da intanet.