Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Najeriya a Yau
Yadda Azumi Ke Inganta Lafiyar Jiki
Use Left/Right to seek, Home/End to jump to start or end. Hold shift to jump forward or backward.
Alumma na yin azumi ne bisa dalilan addini don samun lada kamar yadda Allah ya umurta a cikin Qurani mai girma.
Sai dai daga baya binciken masana kimiyya ya gano cewa bayan lada da ake samu daga yin azumi, akwai wasu alfanu da mai azumi ke samu ga lafiyar jikin shi da suka hada da inganta karfi da zurfin tunani zuwa fitar da gurbatattun abubuwa da jiki baya bukata.
A takaice dai, ba kawai lada mai azumi ke samu ba, har da samun lafiyar jiki da na kwakwalwar sa.
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi Nazari ne kan alakar dake akwai tsakanin yin azumi da kuma lafiyar jikin mutum.